Ci gaba da tsare dakataccen Shugaban EFCC, Abdulrashid Bawa, ba tare da gurfanar da shi kotu ba, har ma da ci gaba da tsare tsohon Gwamnan CBN, Godwin Emefiele duk kuwa da kotu ta bada umarnin a bada belin sa, hakan ya sa an danƙara babbar alamar tambaya kan iƙirarin kishin dimokraɗiyyar da Shugaba Bola Tinubu ke cewa ya na yi.
Fiye da watanni biyu kenan ake tsare da dakataccen Shugaban EFCC, Abdulrashid Bawa a hannun SSS, a Abuja.
Tun a ranar 14 ga Yuni Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi, daga nan kuma SSS suka tsare shi, ba tare da shaida wa duniya irin laifin da ya yi ba. Kuma ba a ce ga dokar da ta bada ikon ci gaba da tsare shi ba tare da gurfanar da shi kotu ba.
Wato kenan dai SSS na tsare da Bawa, tsawon kawanaki 77 kenan bisa umarnin Shugaba Tinubu – watanni biyu har da sati biyu, ba a kai shi kotu ba.
Babban abin ɗaure kai kuwa shi ne, a gefe ɗaya ga Bawa can a tsare, sai Tinubu ya aika da sunan tsohon Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle a matsayin sabbin ministocin sa.
Shi kuma Bawa, dama an dakatar da shi ne tare da kama shi a daidai lokacin da ya ke haƙilon bincikar zargin sace Naira biliyan 70 da Matawalle ya yi.
Sannan kuma wani tsohon Gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu wanda ya taimaka wajen lodi da jigilar biliyoyin daloli lokacin mulkin Abacha su na ɓoyewa ƙasashen Turai, shi ma aka bada sunan sa a cikin sabbin Ministocin Tinubu.
Kai jama’a! Yayin da ake cikin aikin tantance sunayen Ministoci a Majalisar Dattawa, sai kuma Tinubu ya jajirce, ya ɗaure wa tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje gindi, ana naɗa shi Shugaban Riƙo na APC, duk kuwa da cewa har yanzu ba a warware gaskiyar zargin wawurar maƙudan dalolin da aka nuno a bidiyo ya na yi ba.
Kai jama’a! Wai yanzu Ganduje shi ne tauraron kawo canji a APC, jam’iyyar da ta hau mulki a 2015 bisa alƙawarin kawar da cin hanci da rashawa a Najeriya.
Mafi yawan ‘yan Najeriya na kallon naɗa waɗannan mutane da Tinubu ya yi, ɗimbin lada ce ya danƙara wa masu laifi, maimakon ya bari a hukunta su a lokacin da ba su sanye da sulken rigar kariya. Shi kuma mai ƙoƙarin gurfanar da su, sai Tinubu ya yi masa dukan-kabarin-kishiya.
Dama an lura tun daga farkon mulkin Tinubu ya ɓullo da wannan salo na saka wa masu laifi ya naɗa su manyan muƙamai, maimakon a garƙame su. Saboda shi ne ya ɗaure wa tsohon Gwamnan Akwa Ibom, Godswill Akpabio gindi har aka naɗa shi Shugaban Majalisar Dattawa.
Kowa ya san har yau har gobe Akpabio jaɓe-jaɓe ya ke sanye da rigunan zargin satar naira bilyan 108 a lokacin da ya ke Gwamna. Amma a haka tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya kauda kai, ya naɗa shi Ministan Harkokin Neja-Delta.
Babban abin kunya a wancan lokacin, tsohon Shugaban EFCC, Ibrahim Magu na kan binciken Akpabio ne sai tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami ya shirya masa gurungunɗumar da aka cire shi, aka tsare shi, kuma har yau ba a bayyana wa duniya sakamakon rahoton binciken da Gwamnatin Buhari ta yi wa Magu ba.
Kamar Makomar Bawa Kamar Makomar Magu:
Bayan sanarwar da SSS su ka yi cewa Bawa ya kai kan sa hedikwatar su domin a bincike shi, har yau babu wanda ya sake fitowa ko da a cikin mafarki ya shaida wa duniya ga laifukan da ake zargin Bawa ya aikata.
“An gayyaci Bawa ne saboda binciken wasu ababen da ke da alaƙa da shi.” Wannan sanarwar kaɗai ce fa Kakakin SSS, Peter Afunanya ya yi a lokacin. Daga nan kuma shiru ka ke ji.
A ranar Litinin 14 ga Agusta, PREMIUM TIMES ta tuntuɓi Peter Afunanya dalilin ci gaba da tsare Bawa da kuma neman sanin ranar da za a kai shi kotu.
Sai Afunanya ya ce to a tura masa tambayar ta hanyar saƙon ‘tes’. An tura masa, amma har yanzu bai aiko da amsa ba.
Duk Mai Tunanin Tinubu Zai Ceto Dimokraɗiyya Daga Dukan Da Ta Sha, To Mafarki Ya Ke Yi:
Mutane da dama na ganin cewa mafarki ne kawai mutum ke yi idan ma ya na tunanin cewa Tinubu zai ceto ko ya tsaftace dimokraɗiyya daga dattin da shugaban da ya gabace shi ya damalmale ta da shi, to mafarki ne kawai ya ke yi.
‘Tinubu Ya Kashe EFCC Murus, Ba Ta Da Sauran Ƙima’ – Daniel Bwala:
“Tsarin da TInubu ya bi ya kama, ya tsare kuma ya wulaƙanta Bawan EFCC, sannan ya kwashi tulin waɗanda Bawa ke zargi ya naɗa su ministoci wasu ‘yan majalisa, zai kashe EFCC ce murus.” Haka Daniel Bwala, Kakakin Yaƙin Zaɓen Shugaban na PDP, a lokacin zaɓen 2023 ya bayyana.
An sha yin haka a baya. Sai a sauke shugaban EFCC a ce za a bincike shi, amma daga nan shiru ka ke ji.
Tuni dai Babban Lauya Mike Ozekhome ya yi raga-raga da ci gaba da tsare Bawa, ba tare da gurfanar da shi kotu ba, kuma ba a bayyana wa duniya laifin da ya yi ba.
‘Yadda SSS Ke Tsare Mutane Ta Na Take Umarnin Kotu Ke Barazana Ga Dimokraɗiyya, Ba Yujin Mulkin Nijar Ba’ – Mike Ozekhome:
Babban Lauya Ozekhome ya ce SSS ce babbar barazana ga dimokraɗiyyar Najeriya ba juyin mulkin da sojoji su ka yi a Nijar ba.
“Ya kamata Bawa ya kai ƙara kotu a bi masa haƙƙin sa. Idan ma ba shi da lauya, zan iya zuwa na tsaya masa kyauta ba ko sisi. Amma ba zai yiwu a ci gaba da tsare shi haka kawai ba.”
Sai dai kuma wani lauya mai suna Kurtis Adigba ya ce idan ma Bawa ya je kotu, to aikin banza ne, domin ko an ce a sake shi, ya na fitowa a harabar kotu SSS za su iya baɗa wa idon su toka su sake kama shi. Ya ce a ƙasar nan komai na iya faruwa.
Me Ya Sa Ake Ci Gaba Da Tsare Bawa?
Shi dai lauya Adigba ya danganta tsare Bawa da fitowar da ya yi ƙoƙarin binciken Tinubu da Matawalle.
Idan an tuna, a ranar 22 ga Yuni, 2022 lokacin Tinubu ya na takarar shugaban ƙasa, Bawa ya yi wata hira da wata jarida inda ya ce ya na binciken Bola Tinubu.
CIkin Mayu 2023 kuma Bawa ya zargi Matawalle da karkatar da Naira biliyan 70, shi kuma ya zargi Bawa da neman toshiyar bakin dala miliyan 2. Kuma ya ce sai gwamnonin da ke shirin sauka Bawa ke wa barazana. EFCC dai ta ƙaryata zargin.
Har sai da ta kai Matawalle ma cewa, “idan an ce ni ɓarawo ne, to ba wanda zai kama ni har sai an kama sauran ɓarayin tukunna.”
Idan ba a manta ba, sai da Bawa na EFCC ya gayyaci Akpabio a lokacin da ake ta ƙoƙarin cewa shi za a naɗa Shugaban Majalisar Dattawa.
Sannan ɗan taratsi ya kai ƙorafin Tinubu a EFCC, bisa rawar da ya taka a zaɓen 2019, inda ya ciko motocin banki biyu maƙil da kuɗaɗe a jajibirin zaɓe, kuma ba a yi masa komai ba.
Discussion about this post