Kotun Tarayya ta amince da roƙon da Gwamnatin Tarayya ta yi, ta nemi rufe fuskokin masu bada shaida kan Tukur Mamu, bayan hana kowa shiga.
Za a hana shiga cikin mota Kotun, lokacin da ake bayar da sheda kan Mamu.
Ana tuhumar sa da laifin haɗa baki da ‘yan ta’addar da suka yi fashi a cikin jirgin kasa, a cikin 2022.
Mai Shari’a lnyag Ekwo ya bayar da damar gabatar da masu shaidar, bayan lauyan Gwamnantin Tarayya, D.E Laswe ya nemi haka.
Abin Da Zai Faru A Zaman Kotu A Ranar:
1. Za a gudanar da zaman shari’ar ba tare da masu kallo ba, sai wasu manema labarai.
2. Za a rufe fuskar masu bada shaida.
3. Kotu ta amince da ba za a bayyana sunayen masu bada shaida ba, za a yi amfani da wasu sunaye daban.
Lauyan Mamu ya ki amincewa, amma Mai Shari’a ya ɗage zaman zuwa 21 ga wata, saboda ba a gabatar da Mamu ba a ranar.
Daga ranar da aka kama Mamu har yanzu ba a bada belin sa ba.
Discussion about this post