Gwamnan Kaduna Uba Sani a ranar Alhamis ya ce zai rage yawan kudaden da ake kashewa a harkokin gudanar da gwamnati domin bunkasa tattalin arziki da tsaro a jihar.
Sani ya kuma ce kwamishinonin sa da ya nada za su yi amfani da tsoffin motocin su maimakon a siya masu wasu domin rage barnatar da kudaden gwamnati.
Ya ce yanzu lokaci ne na tsimi da tattali da hakan ya zama dole a dauki tsauraran matakai domin a samu ci gaba a jihar.
Gwamnan ya kuma kaddamar da asusu domin tallafawa talakawa musamman a wannan lokaci da ake fama da radadin cire tallafin man fetur.
Ya Kuma ce zai sadaukar da kashi 50% na albashinsa duk wata domin dankarawa a wannan asusu da za a rika taimakawa wa marasa karfi a jihar.
Sani wanda ya yi jawabi a taron rantsar da sabbin kwamishinonin da aka yi a gidan gwamnatin jihar ranar Alhamis ya ce yana da masaniyar cewa jihar kanduna na fama da matsalolin koma bayan tattalin arziki da rashin tsaro.
“ Muna dogaro da kwarewar ku domin kawo karshen matsalolin koma bayan tattalin arziki da rashin tsaro a jihar.
Wannan shawara da gwamna Sani ya dauka ya samu yabo da jinjina daga mutanen jihar cewa lallai yana da kishin talakawa a zuciyar sa.
Wani mazaunin Kaduna, Gambo Awwal, ya shaida wa wakiliyar mu a Kaduna cewa, ” Abinda gwamnan ya yi abune da ya cancanci yabo. Maimakon ya bi ayari wajen kashe makudan kudi a siya sabbin motoci na alfarma ga Kwamishinoni, ya ce tsoffin da suke dashi kowa ya ci gaba da amfani da shi.
” Bayan haka dole a yaba wa gwamna Sani kan asusun tallafi da ya bude don talakawa, da kuma sadaukar da rabin albashin sa duk wata don saka wa a wannan asusu saboda talakawan Kaduna.
Discussion about this post