Gwamnatin jihar Adamawa ta bayyana cewa za tawo ƙarshen matsalar rashin ruwa a fadin jihar.
Sakataren gwamnatin jihar Awal Tukur ya sanar da haka a garin Yola a taron liyafa don karrama tsohon ministan Babban Birnin Tarayya Abuja Mohammed Bello da Shugaban ma’aikatan fadan gwamnati Edga Amos.
Tukur ya ce ruwa na daga cikin muhimman ababen more rayuwa yayin yake tabbatar da cewa gwamnati ta dauki mahimman matakai domin samar da ruwa a jihar.
Ya ce gwamnatin Fintiri gwamnati ce da za ta mai da hankali wajen samar da ababen more rayuwa domin mutanen jihar.
Tukur ya kuma taya ministan murnan yi wa jihar da kasa hidima.
Shugaban kwamitin taron Ibrahim Waziri ya taya Mohammed da Amos murnar kammala aiki lafiya.
Bello ya mika godiyarsa ga mutanen Yola da suka taya shi da addu’o’I yayin da yake aiki.
Ya yi kira ga ma’aikatan gwamnati da su rika kokari a aikin su domin samar da ci gaba a jihar.
Discussion about this post