Gwamnatin Bola Tinubu za ta raba wa sabbin ‘yan Majalisar Tarayya naira biliyan 70, manoma a ba su tallafin naira biliyan 19.
Za a yi masu feshin ruwan a kuɗaɗen domin inganta ayyukan su.
Amma kuma manoma waɗanda suka yi gagarumar ambaliya a 2020, a faɗin ƙasar nan, za a raba masu Naira bilyan 19.
Wannan bayani na ƙunshe cikin wani ƙudirin da Majalisa ta amince da shi a ranar Alhamis.
Ambaliyar 2022 ta ci rayukan mutane 500, ta yi ta’adi a gonaki heta 78,168, ta lalata hekta 70,566.
PREMIUM TIMES ta bada labarin cewa yadda ‘yan Majalisar Tarayya su ka ce albashin su ba ya isar su, har sun fara cin bashi.
Mambobin Majalisar Tarayya sun tayar da ƙurar neman a yi masu albashi mai tsoka, saboda tsadar rayuwa da ake fama.
Ba albashi kaɗai su ka yi magana ba, har ma da alawus-alawus.
Fito da wannan magana ya haifar da ruɗani a zaman Laraba, har Shugaban Majalisar Tarayya Tajuddeen Abbas ya ce a shiga taron musamman.
Daga nan kuma sun ce har yanzu fa ba a biya su albashi da alawus ba, har sun fara cin bashi.
Wanda ya halasci taro, amma ya ce a sakaya sunan sa, ya ce albashi da alawus ɗin ba ya isar su tafiyar da ayyukan su da sauran harkokin su.
Amma kuma ya ce ba a yi maganar albashin su na watan jiya ba.
Shugaban Majalisar Tarayya Tajuddeen Abbas, ya ce maganar albashi mai tsoka, magana ce babba.
Discussion about this post