Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya a ranar Lahadin da ta gabata ta cafke wasu mutane hudu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne, bisa zargin yunkurin kai wa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar hari.
Ofishin yada labarai na Atiku a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin ya ce ‘yan sandan sun kama wani da ake zargi mai suna Jubrila Mohammed, mai shekaru 29, wanda ya bayyana cewa shi dan Boko Haram ne daga Damboa a jihar Borno. Kakakin ‘yan sandan ya kuma tabbatar da hakan.
” Muna sanar da al’ummar Najeriya cewa da misalin karfe 9:44 na dare a ranar Lahadi, 23 ga Yuli, 2023, an kama wani mutum da yayi kokarin kutsawa gidan mai girma Atiku Abubakar a Yola.
“Mutumin da jami’an tsaro suka kama a gidan Atiku Abubakar an mika shi ga ‘yan sanda. “Da ‘yan sanda suka yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya bayyana kansa a matsayin Jubrila Mohammed mai shekaru 29 kuma ya amsa cewa shi dan Boko Haram ne daga Damboa a jihar Borno.
Wanda ake zargin ya kuma sanar da ‘yan sanda cewa shi da abokan aikinsa, wadanda aka kama su ma, sun yi niyyar kai hari kan kungiyoyi masu alaka da Atiku Abubakar da wasu wurare masu muhimmanci a Yola.
“An mika dukkan wadanda aka kama su hudu ga hukumomin soji.
“ Bayan jinjina wa ƴan sanda da muke yi, Muna kara rokon sauran hukumomin tsaro da suma su maida hankali akan haka domin a yi nasarar ci gaba da zaƙulo muggan iri irin waɗannan.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Suleiman Nguroje, ya tabbatar da kama wadanda ake zargin lokacin da wakilinmu ya same su domin jin ta bakinsu.
Nguroje ya ce ‘yan sanda sun mika wadanda ake zargin ga sojoji domin gudanar da bincike saboda (wandanda ake zargi da aikata laifin) ya shafi ta’addanci.
Discussion about this post