Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna Mohammed Jalige, ya bayyana cewa ta yi nasarar kamo yan Iska, barayin waya da ‘yan sholisho 207.
Jalige ya bayyana cewa baya ga barayin waya da aka cafke, jami’an tsaro sun kama wasu da dama masu yi wa mutane rufa ido da katin ATM din su su damfare su.
Idan ba a manta ba makonni biyu da suka wuce Jalige ya bayyana cewa yan sanda sun kama masu tada zaune tsaye a fadin jihar har mutum 503
Jalige ya ce a cikin su an kama yan bindiga, yan iska masu yi wa yan mata fyade, yan Kodin da barayin waya, sannan kuma har bindigogi an kwato a hannun wadanda aka kama.
Discussion about this post