Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ‘yan iska, barayin wayoyin da ‘yan kwaya sama da 500 a jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Mohammed Gumel ya fadi hakaa lokacin da mambobin kungiyar NUJ reshen jihar ta kawo masa ziyara a ofishinsa.
Gumel ya ce baya ga kaurin suna da wadannan bata gari suka yi mutane a jihar na musu kallon ‘yan fashi da makami ne kawai.
Ya ce a dalilin haka ya sa rundunar ta yi gaggawar daukan mataki domin ganin ta kawar da matsalar’.
“Mun samu nasarar rage aiyukan barayin waya a fadin jihar.
“Zuwa yanzu rundunar ta kama batagari irin haka sama da 500 sannan har an yanke musu hukunci.
Bayan haka Gumel ya ce aiyukkan ‘Yan daba na daga cikin matsalolin da rundunar ke fama da su.
“Mun gano ‘Yan daba 16 inda mutum 9 sun amince su hada hannu da mu domin kamo sauran ‘Yan daban dake jihar.
Gumel ya ce gwamnati za ta Gina wa rundunar Ofis tare da zuba kayan aiki na zamani a Dala.
Discussion about this post