Akalla mutum uku sun mutu yayin da wasu da dama suka ji rauni sanadiyyar harin da ‘yan bindiga suka kai kauyen Kamuwa Nyifiye dake karamar hukumar Takum jihar Taraba ranar Lahadi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Abdullahi Usman a ranar Talata ya ce suna zargin maharan Fulani ne makiyaya.
Usman ya ce maharan sun shigo kauyen suna harbi ta ko ina yayin da wasu Kiristoci ke hanyar su ta dawowa gida daga coci.
Ya ce jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda da sojoji sun fatattaki maharan sai dai kuma mutum uku sun mutu sannan wasu sun ji rauni.
Maharan sun Kona gidajen da dama a kauyen.
Bayan haka dagacen kauyen Godson Danlami ya yi kira ga gwamnati da ta hada hannu da jami’an tsaro domin kawo karshen kisan da ake yi a yankin.
Kudancin Taraba musamman karamar hukumar Takum na daga cikin wuraren dake yawan fama da hare-haren ‘yan bindiga da rikicin kabilanci.
Mazauna wurin na zargin maharan ba wasu bane illa Fulani makiyaya amma akwai wasu kangararrun mutane dake aikata muggan aiyukka a yankin da ba Fulani makiyaya ba kawai.
Discussion about this post