Kungiyar dillalan man fetur ta Arewa mai zaman kanta ta ce mambobinta za su tsunduma yajin aiki idan hukumar kula da harkokin man fetur ta Najeriya ta kasa biyan su sama da Naira biliyan 250 da suke bi bashi.
Shugaban kungiyar Musa Maikifi, a wata ganawa da manema labarai ranar Alhamis a Kano, ya ce mambobin kungiyar ma bin gwamnati nashin sama da Naira biliyan 250.
Ya ce waɗannan kuɗaɗe na ake cire wa daga na dakon mai da suke yi zuwa depo depo a jihohin Arewa.
Ya bayyana wuraeren da suke kai mai din sun haɗa da Kaduna, Kano, Suleja, Yola Maiduguri Jos da Gombe.
Maikifi ya yi kira ga gwamnati da shugaban kasa Bola Tinubu da ya saka baki a biya su wannan kuɗaɗe.
Ƙungiyar ta ce za ta fara yajin aiki da hakan zai daɗaɗa gurguntar da harkokin kasuwanci da dada danƙarawa mutanen yakin Arewa azabar raɗadin rayuwa da suke fama da shi sanadiyyar cire tallafi mai da gwamnatin Tinubu ta yi.
Ya ce jinkirin da aka samu na biyan su yana barazana ga sana’o’insu domin wasu ‘ya’yan kungiyar ba za su iya samar da man fetur da kuma sayar da shi ba.
Maikifi ya ce rashin biyan kudin da gwamnati ta yi a kan lokaci zai shafi dakon man fetur din zuwa daukacin jihohin Arewa.
Discussion about this post