Tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya ragargaji waɗanda suka yi adawa da takarar Bola Tinubu da Kashim Shettima a zaɓen shugaban kasa da aka yi a watan Faburairun 2023.
Idan ba a manta ba zaɓen Shettima da Tinubu ya yi a matsayin mataimaki ya tada kura ba kaɗan ba a faɗin kasar nan, inda Kiristocin Najeriya kusan duka suka ja daga da wannan tafiya ta Tinubu da Shettima, wai ba za su yin tafiyar ɗan takara Musulmi, maraimaki Musulmi ba.
Kusan duka kiristocin Najeriya a lokacin zaɓe sun zaɓi Peter Obi ne na jam’iyyar LP wanda ya yi ikirarin cewa takarar sa jihadi ne ga Kiristocin Najeriya.
” Yanzu dai zan ce kurunkus kenan domin ƴan Najeriya sun nuna ba addini ko ƙabilanci bane a gaban su. Abinda ya dame su shine su zaɓi wanda zai share musu hawaye, ya gyara kasa.
Darussa Hudu da zaben Tinubu da Shettima ya koyar da ma su cewa takarar su ba zai yi tasiri ba
1 – Zaɓen Tinubu da Shettima ya kawo ƙarshen zargin da ake yi cewa wai gaggan dakarun Arewa ba za su taɓa bari mulki ya koma kudu ba. Wannan zargi an gama dashi.
2 – Nasarar da Tinubu ya yi a zaɓen da kuma na uku da Peter Obi ya zo duk da tsananin kamfen da aka yi a coci coci domin kiristoci su zaɓe shi, ya nuna wa duniya ashe aikin banza ne kawai suka yi sannan kuma da zaɓen gwaji da suka rika yi a yanar gizo da ke nuna shi ne zai yi nasara, duk ƴar fara ta nuna cewa, makalewa da addini ko ƙabilanci don neman wata kujera aikin banza ne.
3 – Zaɓen Tinubu ya nuna cewa lallai ƴan Arewa na da Alƙawari, idan suka ɗauka za su cika shi koda ko an rubuta shi ko kuma da baki a ka yi shi.
4 – Sannan kuma tatsuniyan da ake yi cewa wai dole wanda za a zaɓa shugaban kasa a Najeriya daga kudancin kasar ya kasance ba musulmi ba ya zama tarihi yanzu domin an gama da hakan, an kakkabe buzu an wuce wurin.
El-Rufai ya kara da cewa ba ,ai yi mamaki ba idan wadanda suka rika sukan takarar Tinubu wai don musulmi ne ko kuma mataimakin sa musulmi suka yi shiru tsit, yanzu da mafi yawa daga cikin waɗanda ya naɗa mataimaka da hadimai Kiristoci ne suka fi yawa, amma ba su fito sun ce wani abu ba.
El-Rufai ya yi wannan jawabi ne a wurin taron kaddamar da wani littafi da bikin yin ritayar shugaban kungiyar MURIC, Ishaq Akintola a Legas.
Discussion about this post