Tsohon gwamnan jihar Kaduna ya bayyana cewa dattawan yankin kudancin Kaduna sun gurza wa mataimakan sa wadanda dukan su ƴan asalin yankin ne rashin mutuncin da bashi misaltuwa.
Sannan kuma El-Rufai ya kara da faɗin dalilan da ya sa ya zaɓi mace musulma ƴar asalin yankin kudancin Kaduna a matsayin mataimakiyar sa.
El Rufa’i ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wani muhimmin jawabi a wajen bikin kaddamar da littafi da ritayar Ishaq Akintola, wanda ya kafa kungiyar kare hakkin musulmi (MURIC) a ranar Asabar a birnin Legas.
” A 2015 da na zaɓi Barnabas Bantex a matsayin mataimaki na, dattawan yankin Kudancin Kaduna, sun nuna bacin ran su matuka, sun rika sukar sa suna yi masa habaici cewa shi mayaudari ne kuma ba shi da amana, kawai wai don ban zaɓi wanda su suke so ba, zaɓin kungiyar Kiristoci na su.
” Sannan kuma wani abu da yake basu haushi shine wai shi ba ya cikin manyan kabilun yankin. Shi Maroa ne, ba Jaba ba, Ko Atyap, Bajju, Ko Kagoro ba, saboda haka bai isa ace wai ƴan kabilar sa ne za azaɓa mataimakin gwamna ba.
” Bari in gaya muku tun ba mu shekara biyu ba Bantex ya bijiro min da zai ajiye aiki, zai hakura da kujerar mataimakin gwamna da yake akai saboda tsananin bala’i da mutanen yankin suka kunno masa. Daga karshe dai ma bayan ya hakura a 2019, rai ya yi halin sa.
“A 2019 ma haka aka yi ta batakashi da waɗannan mutane a lokacin da na zaɓi Hadiza Balarabe, ita ma daga yankin kudancin Kaduna. Haka suka rika yi mata, nuna mata kyama da kiyayya karara.
El-Rufai ya ce haka ya toshe kunnuwan sa ya yi banza da su ya ci gaba da aikin gyara jihar Kaduna. Ita ce mace ta farko da aka zaɓa a matsayin mataimakiyar gwamna a yankin mu na Arewa.
Har El-Rufai ya kammala mulkin sa a Kaduna ba ya ga maciji tsakanin sa da dattawa da mutanen yankin Kaduna.
Discussion about this post