Mazauna garuruwan dake yankin Kananan Hukumomin Maru da Bungudu a jihar Zamfara sun ce duk da cewa an girke jami’an tsaro a yankuna, ƴan bindiga na ci gaba da kai hare-hare a yankunan su.
PREMIUM TIMES ta zanta da mutane kusan goma, ciki har da dan majalisar tarayya mai wakiltar Maru/Bungudu, Abdulmalik Zubairu, kan karuwar hare-haren a yankin.
Zubairu ya ce an kashe mutane sama da 50 a mazabarsa a cikin makonnin da suka gabata sannan wasu da dama sun jikkata.
Dan majalisar ya ce karuwar hare-haren da ake kai wa a yankunan babban abin damuwa ne ga mazauna yankin, manoma da dama da a yanzu ba sa iya shuka amfanin gona saboda barazanar ƴan bindigan.
“ Mahara sun kashe mutum tara a ƙauyen Tungar dake karamar hukumar Bungudu. A ƙauyen Kwaren Tsauni, mahara sun kashe mutane kusan goma. Kuma ka tambaye ni da kanka, a jiya (Laraba), kamar yadda bayanai suka nuna, an kashe mutum tara a Dangulbi yayin da wasu mutum bakwai da suka samu munanan raunuka ke kwance a asibiti. A ranar Laraba har yanzu an kashe wani lauya a gidansa da ke garin Kwatarwkashi. Wadannan abubuwa suna ci gaba da faruwa a kullum,’ in ji shi.
Bayan haka ɗan majalisar ya kara da cewa akwai wasu kauyuka da suka haɗa da Kurar Mota, da Bingi da yanzu haka suna cikin halin ha’ula’i da fargabar yiwuwa dirowar ƴan bindiga.
Wani mazaunin kauyen Dangulbi, Bello Mansur, ya ce an jefa al’ummar cikin rudani da tashin hankali bayan harin da aka kai ranar Laraba.
‘Wadannan mutane sun shigo cikin mu su ka yi kan mai-uwa dawabi da bindigogi. Babu wanda zai iya gaya muku irin laifin da muka aikata wanda ya cancanci irin wannan sakayyar. Yadda kasan dabbobi haka suka mai da mu, su kashe na kashe wa su yi tafiyar su.
Ya ce ‘yan ta’addan shigo kauyen da misalin karfe 10 na dare ranar Laraba bisa kan babura.
A ƙarshe dai rundunar ƴan sanda jihar ta bayyana cewa ba za ta yi ƙasa a guiwa ba wajen ganin ta kawo karshe ta’addanci a fadin jihar.
Discussion about this post