Gwamnan Kaduna Uba Sani ya naɗa Bashir Zuntu, sabon Akanta Janar din gwamnatin Jihar.
Bashir Zuntu, wanda shine tsohon shugaban karamar hukumar Kubau kwararre ne a harkar sarrafa kudi, tsimi da tattali.
Ya yi aiki a wurare da dama sannan ya ilmantu matuka a harkar kuɗi.
Kafin sanar da naɗin Bashir Zuntu, gwamna Uba Sani ya rantsar da sabbin kwamishinoni wanda majalisar jihar ta amince da su.
A jawabin sa bayan kwamishinonin sun sha rantsuwa, gwamnan ya hore su da su yi aiki tukuru domin mutanen jihar, sannan kuma ya gargaɗe su cewa ba zai yi ɗaga wa kowannen su kafa ba muddun yayi wa sa da aikin sa.
Ya ce gwamnatin sa ta saka muhimman manufofi guda 7 da za ta maida hankali a kai, kuma ya hore su da su tabbata duk abinda za su yi ya dace da manufofin wannan gwamnati.
Wadanda suka sha rantsuwar sun hada da, Mohammed Bello, Mainan Zazzau, wanda shine kwamishinan Ilimi na jihar, sai kuma Sadiq Mamman Legas, Kwamishinan Kananan hukumomi da dai sauran su.
Discussion about this post