Tsohon Gwamna Ayo Fayose ya ce adawa ba faɗa da gaba ba ce.
Ya bayyana haka ga manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, bayan ganawar su a ranar Alhamis, a Abuja.
Ya ce har yanzu ya shi ɗan PDP ne, ba fita za ya yi ba.
Ya ce adawa ba faɗa ba ce don haka a daina amfani da adawa domin cikas.
“Ba za mu fice daga PDP ba har abada, amma kuma tilas a yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.”
Matsayar Fayose A PDP Lokacin Zaɓen Fidda Gwani:
“Ɗan Kudu Mu Ke So A Ba Takara, Ba Atiku Ba” -Ayo Fayose:
Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose ya fito ƙarara ya ce Atiku ya ci amanar Wike, don haka ba zai goyi bayan kamfen ɗin sa ba.
Wata gagarimar rigima ta kunno kai a cikin Jam’iyyar PDP, inda tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose ya bayyana cewa Gwamna Nyesom Wike na Rivers da magoya bayan sa kakaf ba za su goya wa Atiku Abubakar baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ba.
A cikin wata tattaunawar musamman da Fayose ya yi da PREMIUM TIMES, Fayose ya ƙara jaddada cewa tabbas Atiku ya ci amanar Wike, don haka Wike da jama’ar sa za su zuba wa Atiku Ido, “tunda ya na ganin cewa shi kaɗai zai iya cin zaɓe, sai ya je ya ci ɗin.”
Fayose ya ce, “bayan Atiku ya yi nasara a zaɓen fidda-gwani, ya je har gida ya nemi haɗin kan Gwamna Wike, kuma ya yi masa alƙawarin zai naɗa shi ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa.
“Kuma da aka kafa kwamitin tuntuɓa wanda zai fito wa Atiku da ɗan takarar mataimaki, kwamitin ya bayar da sunan Wike.
“Amma da aka shiga aka fita, sai Atiku ya wancakalar da Wike, ya ɗauki Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta.
“Atiku bai yi wa Wike mutunci ba. Domin bayan ya ci amanar sa ya ƙi ɗaukar sa mataimaki, ai ya-kamata ya kira Wike ya sanar da shi dalilin da ya sa ya karya alƙawarin da ya yi, wato ya ba shi haƙuri, amma Atiku bai yi hakan ba.”
Fayose ya ce har yau ya na na nan kan ra’ayin sa cewa kudu ya kamata ya yi mulki ya koma kudu a 2023.
Discussion about this post