Shugaba Bola Tinubu ya kafa dokar-ta-ɓaci kan tsadar abinci, za a ƙayyade farashi, a raba taki, a share dazuka domin faɗaɗa noma a ƙasar nan.
Hakan ya zo ana cikin fama da tsadar rayuwa da tsadar abinci wadda ba a taɓa ganin faruwar haka ba a baya.
Babban Daraktan Yaɗa Labarai Dele Alake ya fitar da sanarwar a taron sa da manema labarai a ranar Alhamis.
“Shugaban ƙasa ya damu da halin da ake ciki a yanzu, musamman tsadar rayuwa da tsadar abinci, da yadda ya ke shafar rayuwar talakawa da marasa galihu.”
Cire tallafin fetur ya tayar da farashin kayan masarufi da kayan amfani.
Tsadar rayuwa da tsadar abinci sun yi tsakani sosai musamman a cikin 2023.
Dele Alake ya ce daga cikin tsare-tsaren da za a fito da su domin shawo kan matsalar, akwai sha yanzu-yanzu da kuma waɗanda a gaba za a ga amfanin da za su yi.
Bola Tinubu ya ce za a faɗaɗa noma sosai, musamman na fadama, domin a bar dogaro da ruwan sama kaɗai.
Za a raba wa manoma abinci ta taki, domin rage masu raɗaɗin cire tallafin fetur.

Za a fito da Hukumar ƙayyade farashi, da tsare-tsare da waɗanda ya ce ba da daɗewa ba za a ta fara.
Discussion about this post