Gwamnonin ƙasar nan sun tabbatar cewa za su gaggauta samar wa talakawa tallafin rage masu raɗaɗin tsadar rayuwa, bayan cire tallafin fetur da aka yi, wata ɗaya da ya wuce.
Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya bayyana haka, bayan tashin su daga taron da su ka yi da Shugaba Bola Tinubu, ranar Alhamis a Legas.
Ya ce Gwamnoni za su taya Gwamnatin Tarayya fitar da al’ummar ƙasar nan daga wahalhalu.
‘Yan Najeriya na fama da matsanancin ƙuncin rayuwa, bayan Buhari, tsohon shugaban da aka zaɓa don ya sauƙaƙe tsadar fetur, kayan abinci da masarufi, amma su ka nunnunka a zamanin sa.
Yayin da ya rage saura makonni biyu kaɗai su ka rage wa Shugaba Muhammadu Buhari kan mulki, ‘yan Najeriya ba za su manta tarihin gwamnatin sa ba, ta yadda za su riƙa tunawa gwagwarmayar faɗi-tashin da su ka riƙa yi har su ka zaɓe shi ya zama Shugaban Ƙasa, bisa kyakkyawar fata da zato da yaƙinin samun sassaucin ƙuncin rayuwa.
Sai dai kuma bayan ya shafe shekaru takwas kan mulki, kusan za a iya cewa babu kayan da aka samu rangwame, sai ma tsadar farashin da kayayyakin su ka riƙa nunkawa.
Buhari kafin hawan sa, ya riƙa haramta biyan tallafin fetur, ya na cewa sata ce. Amma kuma ya ƙarke a Shugaban Ƙasa wanda ya fi saura na bayan sa biyan kuɗin tallafin fetur.
Najeriya na biyan Naira biliyan 400 duk wata a matsayin tallafin fetur, kamar yadda Shugaban NNCPL, Mele Kyari ya bayyana watannin baya.
Kayan abinci sun yi tsadar da bayyana farashin su a nan ɓata lokaci ne, domin talakan da abin ya fi shafa, ya fi kowa sanin tsadar da kayan abincin ya yi.
Buhari ya hau mulki lokacin da ake kuka cewa Naira 850,000 ta yi tsada ga tafiya aikin Hajji. Sai dai kuma maimakon a samu rangwame, Buhari zai sauka ya bar kuɗin tafiya aikin Hajji Naira miliyan 2.95, wato kaɗan ke babu a naira miliyan 3.
An zaɓi Buhari a 2015, lokacin farashin sabulun ‘Crusader’ wanda mata ‘yan ƙwalisa ke wanka da shi ya na Naira 180, wasu wuraren kuma Naira 200. Sai dai kuma Buhari zai sauka a daidai lokacin da ‘Crusader’ ke Naira 1,150, wasu manyan kantinan ma har N1,200.
Discussion about this post