Mambobin Majalisar Tarayya sun tayar da ƙurar neman a yi masu albashi mai tsoka, saboda tsadar rayuwa da ake fama.
Ba albashi kaɗai su ka yi magana ba, har ma da alawus-alawus.
Fito da wannan magana ya haifar da ruɗani a zaman Laraba, har Shugaban Majalisar Tarayya Tajuddeen Abbas ya ce a shiga taron musamman.
Daga nan kuma sun ce har yanzu fa ba a biya su albashi da alawus ba, har sun fara cin bashi.
Wanda ya halasci taro, amma ya ce a sakaya sunan sa, ya ce albashi da alawus ɗin ba ya isar su tafiyar da ayyukan su da sauran harkokin su.
Amma kuma ya ce ba a yi maganar albashin su na watan jiya ba.
Shugaban Majalisar Tarayya Tajuddeen Abbas, ya ce maganar albashi mai tsoka, magana ce babba.
Discussion about this post