Shugaba Bola Tinubu ya jingine harajin 5% da Gwamnatin Tarayya ke amsa a kayan sadarwa da motocin da ake shigowa da su cikin kasar nan.
Dama waɗannan harajin sabbinu shigowa ne, ba su daɗe ba.
Haka kuma an cire harajin goran roba da kwalabe na roba.
Bola Tinubu ya tsayar da amsar harajin 5% a kayan da ake yi a cikin gida.
K
Wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Shugaba ya sa wa hannu ya fitar a ranar Alhamis, Dele Alake ya ce Shugaba Bola Tinubu ya aje Sabuwar Dokar Harajin Motocin hawa da motocin haya.
Ya ce Bola Tinubu ya cire harajin don a samu ragowa a gidajen da ake amfani da.
Shugaban ƙasa ba zai ɗora wa ‘yan Najeriya wata wahala, bayan ta wadda su ke gaganiya da ita ba a yanzu.”
Sanarwar ta kuma ce Bola Tinubu ya lura cewa wasu dokoki daga baya aka fito da su, bayan fara amsar harajin da daɗewa.
“An gusa da amsar harajin zuwa gaba, du da cewa an yi Dokokin da farko da manufar samun tara kuɗaɗe.
Sabuwar Dokar Kuɗaɗe za ta fara aiki daga 1 Ga Satumba, 2023 ba daga Maris ba.
Sai Dokar ETVAO ta tashi daga 27 Ga Maris, 2023 zuwa 1 Ga Agusta, 2023.
Discussion about this post