Shugaban ƙasa Bola Tinubu na so a canja tsarin dakaru yadda za su iya kakkaɓe ta’addanci a Tafkin Chadi.
Ya ce ta haka ne kawai ƙasashen Tafkin Chadi za su yi azamar samun damar yin nasara a kan masu hare-haren ta’addanci, waɗanda suke yawan sake wuraren zama da tashi daga can zuwa nan.
Ya ce dole fa sai an tashi tsaye, musamman cewa masu ta’addanci ba sa daraka Dokoki da Ƙa’idojin amfani da makamai.
Da ya ke bayani a Taron Yaye Zaratan Kwas lamba 45, Makarantar Horas da Zaratan Sojoji, Bola Tinubu ya ce akwai buƙatar a sake shiri sosai domin yaki da masu ta’addanci.
Ya gode wa zaratan sojojin Najeriya, Chadi da Kamaru, ya ce Afirka ta tashi don ta kawar da barazana.
Yayin da ya ke ci gaba da yin la’akari da irin halin da ake ciki, Bola Tinubu ya roƙi a daddage a ceto yankim.
Discussion about this post