Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa shirye-shrye da gwamnatin tarayya ta yi don warware matsalolin rashin tsaro da tsadar rayuwa suna tafe, ba da daɗewa ba.
Ya ce musamman za shi bada muhimmanci a Arewa maso Gabas.
Haka ya bayyana wa manema labarai a ranar Lahadi, a birnin a Kano, lokacin da ya ke ziyarar ta’aziyya.
Shettima tare da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, su ka kai ziyarar rasuwar Abubakar Galadanci.
Da ya ke magana kan matsalar tsaro a yankin Arewa maso Yamma, ya ce ” Nan ba da daɗewa ba gwamnatin Tinubu za ta fito da shiri kan magance matsalar.”
Bayan ganawar sa da Gwamna Abba Kabir, Shettima da tawagarsa su ka zarce Bichi, domin ta’aziyya ga Sarki Nasiru Ado, a madadin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.
Daga Kano, mataimakin shugaban kasar ya sake zuwa Katsina domin yin ta’aziyya ga fitaccen dan kasuwa Dahiru Mangal bisa rasuwar matarsa ta farko, Aisha Dahiru, wadda ta rasu da yammacin Asabar a Abuja bayan gajeruwar rashin lafiya.
An yi jana’izar Mrs Mangal kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Sauran ‘yan tawagar mataimakin shugaban kasa sun hada da dan majalisar wakilai daga Kano, Abdulmumin Jibrin da kuma babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin siyasa, Ibrahim Masari.
Discussion about this post