Tsohon Mataimakin Shugaban APC na Arewa maso Yamma, Salihu Lukman, ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ba ya da ikon da zai iya naɗa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban riƙon APC.
Lukman wanda ya sa sauka a fusace, ya ce Sashe na 31.5 na dokar APC, ya ce Shugabannin APC na Nasarawa ne ke da alhakin a naɗa wa APC Shugaba.
PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Shugabannin Arewa maso Yamma sun amince da Ganduje
Shugabannin APC na Arewa maso Yamma sun amince da
Ganduje a matsayin shugaban riƙo.
Shugabannin daga jihohin Zamfara, Sokoto, Katsina, Kebbi, Kano da kuma Kaduna, sun bayyana wannan goyon bayan a taron da su ka yi a Kaduna.
Cikin wata sanarwar da suka gabatar wa
manema labarai a ranar Laraba, Shugabanin su bakwai cewa suka yi tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ne zai dace da shugabancin APC.
Akwai lsa Acida daga Sokoto, Tukur Ɗan Fulani, daga Zamfara, Abubakar Kana da wakilan Kano, Katsina, Kaduna da Jigawa.
Abdullahi Ganduje ya yi Gwamna tsawon shekaru takwas daga 2015 zuwa 2023 a Kano.
A cikin sanarwar, wadda ke ɗauke da sa hannun su, sun ce Ganduje ya yi gagarimin aiki a lokacin zabe Shugaban Ƙasa, a 2023.
Ta tabbata cewa APC ta fito da wanda zai maye gurbin Abdullahi Adamu, yayin da Shugabannin APC na Arewa maso Yamma sun amince da Ganduje a matsayin shugaban riƙo.
Shugabannin daga jihohin Zamfara, Sokoto, Katsina, Kebbi, Kano da kuma Kaduna, sun bayyana wannan goyon bayan a taron da su ka yi a Kaduna.
Cikin wata sanarwar da suka gabatar wa manema labarai a ranar Laraba, Shugabanin su bakwai cewa suka yi tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ne zai dace da shugabancin APC.
Discussion about this post