Tsohon Gwamna Ayo Fayose ya jaddada cewa ran sa za ta ɓaci sosai matsawar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ƙi naɗa Wike Minista.
Ya ce dole Shugaban Ƙasa ya bayyana godiyar sa ga Gwamnonin G5 na PDP, waɗanda suka tsaya domin tabbatar da adalci a zaɓen ɗan kudancin Najeriya.
Haka Fayose ya bayyana a wata tattaunawa da ya yi da Gidan Talabijin na Channels TV, a ranar Lahadi.
“Tsohon Gwamnan Ribas ya zama mai so a yi adalci da gaskiya.
“Ya tabbatar da ɗan takarar shugaban kasa daga kudu ya yi galaba a APC.”
Fayose ya gana da Tinubu a ranar Alhamis, ya ce ba zai bar PDP ba.
Tsohon Gwamna Ayo Fayose ya ce adawa ba faɗa da gaba ba ce.
Ya bayyana haka ga manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, bayan ganawar su a ranar Alhamis, a Abuja.
Ya ce har yanzu shi ɗan PDP ne, ba fita zai yi ba.
Ya ce adawa ba faɗa ba ce don haka a daina amfani da adawa domin kawo cikas.
“Ba za mu fice daga PDP ba har abada, amma kuma tilas a yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.”
Discussion about this post