Sojojin Najeriya sun ragargaza matatun mai 30 da tankuna 125 a Neja Delta.
Hedkwatar Tsaro ce ta bayyana cewa sojoji sun samu wannan gagarimar nasara a kwanakin baya.
Wuraren da aka lalata ɗin a Neja Delta su ke.
Abdullahi Ibrahim ya bayyana haka a madadin Daraftan Yaɗa Labarai.
Ya yi bayani a wurin taron manema Labarai.
Ya ce an lalata wurare 227, jirage 21 samfurin m Kwale-kwale.
Sojoji sun kama lita Miliyan 1.675 ɗanyen mai, lita 74,500 gas, motoci 10, babura 20, muggan makamai 8, harsashi 330.
An cafke masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa har 42.
A waɗansu farmaki an harbe ‘yan lPOB 4, an tafi da muggan makamai da sauran su.
Discussion about this post