Wasu sojojin kasar Nijar sun fito gidan talabijin na ƙasar suka tabbatar da juyin mulki a kasar wanda suka yi.
Wanda ya yi magana a madadin sojojin da suka yi juyin mulkin Manjo Ahmadou Abdrahamane ne ya sanar da juyin mulkin a Talabijin ɗin Kasar.
Sun sanar da rushe kundin tsarin mulkin ƙasar, sannan kuma sun kulle duka iyakokin ƙasar baki ɗaya har da sauka da tashi daga filin jirgin saman kasar.
Sai dai kuma har yanzu ba a san ko a wani hali shugaban kasar ya ke ciki ba Mohamed Bazoum.
Sojojin sun bada dalilin yin juyin mulkin cewa wai saboda halin da Nijar ke ciki ne na taɓarɓarewar tsaro da tattalin arziƙi and kuma tabarbarewar shugabanci.
A halin yanzu babu fita ba shiga ƙasar Nijar, hatta shugaban kasar Benin da ECOWAS ta tura kasar bai iya ganawa da shugaban sojojin da suka kwace mulki a kasar ba.
Discussion about this post