Hedikwatar tsaron Najeriya DHQ ta bayyana cewa sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda 59, sun kama wasu 88, masu garkuwa da mutane 10, ‘yan bindiga 20 da mutum 19 a cikin mako daya.
Darektan yada labarai na hedikwatar tsaron Edward Buba ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar ranar Juma’a.
Buba ya ce a tsakanin wannan lokacin dakarun sun ceto mutum 88 da mahara suka yi garkuwa da su.
Ya ce sojoji sun kama bindigogi 68 da harsasai 1,364 da suka hada da bindigogi kirar AK-47 guda 26, bindiga kirar GPMG daya, bindiga kirar AKMS daya, bindiga kirar FN daya, Pump action hudu, gajerar bindiga ‘pistol’ biyar da bindigan farauta 19.
Sauran kayan da jami’an tsaron suka kama sun hada da man fetur lita 323,650, AGO lita 128,700, lita 4,000 na DPK da kudi N388,441,660.00.
Bayan haka Buba ya ce dakarun dake aiki a karkashin ‘Operation Hadin Kai’ a Arewa maso Gabas sun kashe mahara da dama, sun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su kuma sun kama makamai a harin da suka kai kananan hukumomin Gwoza, Konduga, Bama da Mafa.
Ya ce a dalilin wannan hari ‘yan ta’adda da dama sun mika wuya sannan dakarun sun kama wasu masu siyar da makamai a Yobe.
Buba ya ce dakarun sun kashe ‘yan ta’dda 13, sun kama wasu 12 sannan sun ceto mutum 18 da aka yi garkuwa da su.
‘Yan ta’adda 746 da suka hada da maza biyu, mata 336 da yara kananan 426 na daga cikin wadanda suka mika wuya.
Buba ya ce ‘Operation Safe Haven’ dake Arewa ta Tsakiya sun kai wa mahara hari a maboyar su dake kananan hukumomin Logo, Takum, Ukum dake jihohin Benue da Taraba.
Ya ce dakarun sun kashe ‘yan ta’adda da dama, sun kama wasu, sun ceto wasu mutane da aka yi garkuwa da su tare da kama makamai.
Daga nan Buba ya ce dakarun sun kama batagari da makamai a kananan hukumomin Lere da Sanga a jihar Kaduna.
Ya ce dakarun dake aiki a karkashin ‘Operation Whirl Stroke’ sun kai hari maboyar mahara dake Wukari, Ukum, Logo da Takum a jihohin Benue da Taraba.
Buba ya ce jami’an tsaron sun kama barayin shannu da ‘yan ta’adda a Guma na jihar Benue da masu siyar da makamai mutum 7 a Doma a jihar Nasarawa inda suka kama makamai da dama daga hannun su.
A Arewa maso Yamma Buba ya ce ‘Operation Hadarin Daji’ sun ceto mutum 50 da aka yi garkuwa da su a kananan hukumomin Talatan Mafara da Maru dake jihar Zamfara.
Ya ce dakarun sun kashe mahara biyar a jihohin Katsina, Zamfara da Sokoto.
Buba ya ce rundunar sojin sama dake aiki a karkashin ‘Operation Hadarin Daji’ sun yi wa mahara ruwan bamabamai a mabuyar su dake Sola inda suke kama mutane a hanyar Jibia zuwa Katsina a jihar Zamfara.
Ya ce maharan sun kashe ‘yan ta’adda 13, sun kama bindiga kirar GPMG guda daya, manyan bindigogi kirar AK-47 guda 3, bindiga kirar PKT guda daya, bindiga kirar FN daya, bindiga kirar hannu, bindigan farauta goma,da wasu makamai.
Saura sun hada da babura 12, Keke NAPEP biyu, wayoyin salula 6, adda 6, rediyo karama daya, rediyo mai amfani da na’urar Sola daya, diga daya da kibiya guda 12.
“Dakarun sun kama masu hada baki da ‘yan bindiga guda uku Kuma sun ceto mutum 75 da aka yi garkuwa da su.
Discussion about this post