Jam’iyyun marasa rinjaye na majalisar Dattawa sun zabi Simon Mwadkwon daga jihar Filato a matsayin shugaban marasa rinjaye na majalisar Dattawa.
Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya ksa ya tsare don ya zama shugaban marasa rinjaye na majalisar amma hakan bai yiwu masa ba.
An zabi Oyewunmi Olalere daga jihar Osun a matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye, sai kuma Darlington Nwokeocha daga jihar Abia, a matsayin Bulalalar majalisa, sai Sanata Rufai Hanga na jam’iyyar NNPP mataimakin Bulalar majalisar Dattawa.
An zaɓi tsohon Gwamnan Ebonyi, Sanata Dave Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, yayin da Sanata Ndume daga Jihar Barno ya zama Bulaliyar Majalisar Dattawa.
Sanata Lola Mataimakin Bulalar Majalisa.
An amince da su ba tare da wata jayayya ba, a matsayin waɗanda jam’yyar APC ta amince da su.
An zaɓe su wata ɗaya bayan Akpabio ya zama Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin kuma mataimakin sa.
Sabuwar Majalisar Dattawa ta 10 ta zaɓi Sanata Godswill Akpabio daga jihar Akwa Ibom sabon Shugaban Majalisar Dattawa.
Sanata Barau Jibrin daga Jihar Kano aka zaɓa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.
Akpabio ya fito daga Kudu maso Gabas, shi kuma Barau Jibrin daga Arewa maso Yamma.
Akpabio ya kayar da Sanata Abdul’aziz Yari daga Jihar Zamfara, inda ya samu ƙuri’u 63, shi kuma Yari 46.
Discussion about this post