Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta gama gabatar da hujjojin ta halasta nasarar da ɗan takarar APC, Bola Tinubu ya yi a zaɓen shugaban ƙasa
A ranar Talata ce lNEC ta gabatar wa kotu babban jami’in lCT Lawrence Boyode
Lauyan INEC Abubakar Mahmoud ya gabatar da shi ya yi rantsuwa, sannan ya gabatar da takardu masu bayanan Shettima ya janye daga takarar sanata sannan ya tsunduma babbar.
A ranar Litinin ma, rashin bayyanar mai bada shaida ya kawo tsaiko ga kare sahihancin nasarar Tinubu da lNEC ta fara
A ranar Litinin Hukumar Zabe ta Kasa ta fara kare nasarar da ta ce ɗan takarar shugaban kasa a APC, Bola Tinubu ya samu a zaɓen shugaban ƙasa.
Amma kuma rashin bayyanar mai bada shaida ya kawo tsaiko a kare sahihancin nasarar wadda ya dace a ce an gabatar da mai bayar da shedar.
Lamarin ya faru a shari’ar da ake yi tsakanin Peter Obi na LP da APC, Bola Tinubu da kuma Shettima da lNEC a ɗaya ɓa
ngaren.
Peter Obi ya rufe gabatar da shaidu, ya rage wa lNEC ta tabbatar da sahihancin zaɓe
Rashin wanda zai bada sheda ya haifar da rashin fara karewar a ranar Litinin.
Lauyan INEC Abubakar Mahmoud ya sanar wa Shugaban Alƙalan, Harna Tsammani rashin zuwan wanda zai bada shedar.
Lauyan Peter Obi ya nuna rashin jin daɗin sa, har ya ce ya dace a sanar da su tun kafin ranar zuwa kotu.
Lauyan INEC ya nemi a ɗage shari’ar zuwa Talata, washegari.
Discussion about this post