A ranar Litinin Hukumar Zabe ta Kasa ta fara kare nasarar da ta ce ɗan takarar shugaban kasa a APC, Bola Tinubu ya samu a zaɓen shugaban ƙasa.
Amma kuma rashin bayyanar mai bada shaida ya kawo tsaiko a kare sahihancin nasarar wadda ya dace a ce an gabatar da mai bayar da shedar.
Lamarin ya faru a shari’ar da ake yi tsakanin Peter Obi na LP da APC, Bola TInubu da kuma Shettima da lNEC a ɗaya ɓa
ngaren.
Peter Obi ya rufe gabatar da shaidu, ya rage wa lNEC ta tabbatar da sahihancin zaɓe
Rashin wanda zai bada sheda ya haifar da rashin fara karewar a ranar Litinin.
Lauyan INEC Abubakar Mahmoud ya sanar wa Shugaban Alƙalan, Harna Tsammani rashin zuwan wanda zai bada shedar.
Lauyan Peter Obi ya nuna rashin jin daɗin sa, har ya ce ya dace a sanar da su tun kafin ranar zuwa kotu.
Lauyan INEC ya nemi a ɗage shari’ar zuwa Talata, washegari.
PREMIUM TIMES ta bada labarin Atiku da Peter Obi sun kammala gabatar wa kotu shaidu da lodin kwafe-kwafen hujjoji, saura jiran hukunci.
A ranar Juma’a ce Atiku Abubakar da Peter Obi su ka kammala gabatar wa Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa shaidu da kuma tulin hujjojin su.
Yayin da Atiku ya gabatar da masu shaida 27, Peter Obi ya gabatar da 13.
Haka a ranar Juma’a ɗin Atiku ya gabatar da kwafen bayanan Jami’ar Jihar Chicago.
Discussion about this post