Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC ta ce masu bada shaida 24 ga Atiku taron-yuyuyu ne, domin ysun gaza bayyana wuraren da su ka ce an yi maguɗi a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Shi dai ɗan takarar shugaban kasar a PDP, da farko cewa ya yi zai gabatar da shaidu 100, kuma 27 kaɗai ya gabatar.
PDP da Atiku zarge-zargen harƙalla ce su ka yi a zaɓen, amma kuma lauyan INEC, Abubakar Mahmoud, ya sanar wa kotu cewa a cikin rumfar zaɓe 176,000, masu ba da shaida 24 kaɗai ya iya gabatar wa kotu.
Saboda haka ya ce masu ba da shaida 24 ba su iya bayar da shaidar abubuwan da suka faru a faɗin ƙasar nan ba.
“A bisa doka, tilas PDP ta kawo shaida daga mazaɓa fiye da 176,000 da ke cikin ƙasar nan, domin bayar ba’asin yadda aka yi maguɗin da Atiku ya ce an yi.
Shi ma Shugaban Ƙasa BolacTinubu, cewa ya yi bayanan Atiku cike su ke da ruɗani, shaci-faɗi da soki-burutsu.
Lauyoyin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu sun bayyana
wa Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa cewa bayanan Atiku Abubakar ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, cike su ke da ruɗani, shaci-faɗi da soki-burutsu.
Dalilin haka ne su ka ce a yi watsi da bukatar Abubakar, da ke so a soke zaɓe ko a ba shi nasara.
Wole Olanipekun, a madadin Bola Tinubu, ya roƙi cewa PDP da Atiku ɗan takarar ta sun gaza gabatar da shaidu da lodin harƙallar da su ka yi zargi a zaɓen 2023.
“Ba komai a zarge-zargen PDP da Atiku, daga soki-burutsu sai shirme.”
Da ya koma kan Peter Obi, Wole Olanipekun ya ce masu cewa a soke zaɓe don Bola Tinubu bai
samu kashi 25% a FCT Abuja ba, molon-ka ne.
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana wa Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa cewa soke zaɓe don ba shi samu kashi 25% a FCT Abuja ba, molon-ka ne.
Ya bayyana haka a cikin rubutaccen ba’asi da ya yi na ƙarshe a shari’ar sa da Peter Obi na LP.
Ya ce FCT Abuja daidai ce da sauran jihohi, saboda haka batun soke zaɓe bata lokaci ne.
Peter Obi na LP ya garzaya kotu ya nemi kotu ta soke zaɓen Shugaban Ƙasa, saboda Bola Tinubu ya rasa samun 25% a FCT Abuja, da wasu dalilai.
Doka ta ce wanda ya yi nasara ya zama ya samu ƙuri’u ɗaya bisa ga uku na wasu jihohi, har da FCT Abuja.
Amma shi Obi ya ce tsarin mulkin Najeriya cewa ya yi tilas sai da FCT Abuja.
A bayanan Bola Tinubu da Wole Olanipekun lauyan Bola Tinubu ya gabatar, ya ce 25% a FCT Abuja ba dole ba ce.
Ya bayar da Sashe na 134 2b, ya ce a sashen babu wani wuri da aka ce lallai sai da FCT Abuja.
Shi ma ɗan takarar PDP, Abubakar ya garzaya kotu, ya nemi a soke zaɓen.
Discussion about this post