Kotun Koli da kuma APC, sun ƙaryata zargin Tinubu ya kira Babban Alƙalin Tarayya ta waya, har suka yi taɓo yadda shari’ar zaɓen Shugaban Ƙasa za ta iya kaiwa.
An yi zargin Bola Tinubu ya kira Olukayode Ariwoola ta waya.
A cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labarai na Kotun Ƙoli ya fitar, ya ƙaryata zargin cewa Bola Tinubu ya nemi Ariwoola ya sa hannu Yadda Kotun Ɗaukaka Ƙarar Zaɓen Shugaban Ƙasa ba ta soke zaɓen 2023 ba.
Ariwoola ke da alhakin bada hatta waɗanda za su yi shari’a a Kotun koli.
Ya ga dama ya naɗa wani ko shi da kan sa ya Shugabanci masu Shari’a.
Festus Akade, ya ce Ariwoola bai yi wata waya da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ba.
Daga nan ne kuma ya ce zargin Ariwoola ya yi waya da Shugaban SSS, ƙarya ce.
Ya ce shari’ar a fili a ke gudanar da komai.
Ya yi gargaɗin a daina amfani da kafafen watsa labarai ana watsa labaran karya.
Shi kuma Kakakin APC, Felix Morka, ya ce masharranta kuma marasa gaskiya su ke yaɗa labarai irin haa da basu da tushe.
Kada a manta, a cikin Maris an yi zargin cewa Ariwoola ya gana da Bola Tinubu a Landan. Amma a lokacin ya fito ya ƙaryata. Haka.
Discussion about this post