Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa nan gaba za ta sanar da Jam’iyyu ranar da za su bayar da ba’asin rufe batutuwa a gaban masu sauraren shari’a.
A ranar Alhamis, lauyan APC Lateef Fagbemi ya ce ya gama ga gabatar da hujjojin wanke Nasarar da Tinubu da APC, saboda “cigaba da ragargazar ɗan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ba shi da ɓangaranci da jibgar mataccen doki.”
Tinubu ya gabatar da takardar wanke shi daga zargin safarar muggan ƙwayoyi Amurka.
A ranar Laraba ce Shugaba Bola TInubu ta hannun lauyoyi ya gabatar wa kotu shaidar yadda ya ce ofishin Jakadancin Amurka ya wanke shi daga zargin aikata laifuka a can ƙasar.
Bola Tinubu ya bayar da satifiket na shaidar gama ‘degree’ a America.
Wole Olanipekun ya gabatar da takardun a ranar Talata.
Cikin 2003 tsohon shugaban ‘yan sanda Tafa Balogun ya rubuta wa Ofishin Jakadancin Amurka cigiyar taɓa samun Bola Tinubu da laifi, amma ba a same shi da laifin ba.
Zarge-zargen Da Bola Tinubu Za Ya Warware Wa Masu Shari’a:
Gadangarƙamar harƙallar muggan ƙwayoyi, rufa-rufar asalin iyaye da kakanni sun zama jibadau, kayan nauyin da Tinubu ya kasa sauke wa kan sa.
Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin PDP, Atiku Abubakar, ya shaida wa kotu cewa Zaɓaɓɓen Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya jibga wa kan sa alkyabba mai ɗauke da dattin muggan ƙwayoyi, wadda kuma ta hana kowa ya iya tantancewa ko tabbatar da tushe, asali da haƙiƙanin mahaifar sa.
Atiku da PDP na ƙalubalantar nasarar da Tinubu ya samu a zaɓe. Sun garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa a Abuja. Kuma zargin tu’ammali da muggan ƙwayoyi na cikin hujjojin da su ka baje wa kotu a faifai.
A zaɓe dai Tinubu ya samu ƙuri’u 8,794,726, shi kuma Atiku 6,984,540.
Amma kuma Atiku ya zargi INEC da Tinubu da tafka harƙalla da ƙin bin ƙa’idojin da ke shimfiɗe a cikin Dokar Zaɓe a lokacin tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa, a ranar 25 ga Fabrairu.
‘Tarihin Faɗuwa Zaɓe Kaɗai Atiku Ya Kafa A Siyasa’ – Tinubu:
Tinubu a raddin sa a kira Atiku ɗan siyasar da faɗuwa zaɓe ya zama rigar sa ta wankan shiga jama’a. Ya ce tun 1993 Atiku ke yunƙurin zama shugaban ƙasa, amma bai yi nasara ba, ga shi har wuri ya ƙure masa a 2023.
‘Tarihin Siyasa Na Ya Fi Na Wanda Amurka Ta Ƙwace Wa Dukiya Saboda Tu’ammali Da Muggan Ƙwayoyi’ – Raddin Atiku Ga Tinubu:
A cikin bayanan da Atiku ya baje wa kotu a faifai, ya ce shi dai ya shiga takarar shugaban ƙasa ba tare da gulando ko dagwalon dattin wata gadangarƙamar muggan ƙwayoyi da ɓoyon asali ko rufa-rufar wuraren da ya yi karatu, kamar yadda Tinubu ya yi ba.
Yanzu dai abin da ya rage shi ne a fara sauraren ba’asi daga ɓangarorin lauyoyin.
Tsohon Shugaban Ƙasa ya ce har yau har gobe bai taɓa ɓoye ina ne asalin ko shi wane ne ba, kuma bai taɓa baddala wuraren da ya yi karatu ba.
‘Doka Ta Haramta Wa Tinubu Takara Saboda Kama Shi Da Laifin Tu’ammali Da Muggan Ƙwayoyi A Amurka’ – Atiku:
Atiku ya kai wa kotu lodin hujjojin cewa Dokar Najeriya ta haramta wa Tinubu takarar shugaban ƙasa, saboda an taɓa kama shi da laifin Tu’ammali da muggan ƙwayoyi a Amurka, har aka ƙwace masa dukiya.
A cikin ƙarar da ya shigar, Chris Uche (SAN) wanda shi ne babban lauyan Atiku, Amurka ta karɓe dala 460,000 daga hannun Tinubu, a matsayin yarjejeniyar da ta hana a garƙame shi a gidan kurkuku, bayan an kama shi da muggan ƙwayoyi a ƙasar.
Zargin Tinubu Na Ɗauke Da Katin Zama Ɗan Ƙasar Guinea:
Atiku ya shaida cewa takarar shugaban ƙasa a Najeriya ta haramta kan Tinubu, saboda ya na da katin zama ɗan ƙasar Guinea, ga shi kuma ɗan Najeriya. Ya ce Dokar Najeriya ta haramta wa mai ɗauke da wani katin wata ƙasa haɗe da na Najeriya, ba zai yi takarar shugabancin Najeriya ba.
Baya ga wannan, Atiku da PDP sun shaida wa kotu cewa Tinubu ya kasa yi wa INEC cikakken bayanin wuraren da ya yi karatu daga farko har ƙarshe, a cikin Fom mai lamba EC9 na INEC da ya cike. Hakan kuwa ya karya dokar Najeriya ce ƙarara.
Atiku ya ce Tinubu tubalin toka ne, ga mutum har mutum, amma kowa na shakku da tababar haƙiƙanin yawan shekarun sa. An kasa gane haƙiƙanin jihar da aka haife shi, ana rufa-rufar waɗanda su ka haife shi, kuma ƙumbiya-ƙumbiyar wuraren da ya yi karatu.”
Discussion about this post