Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a PDP, Atiku Abubakar, ya zargi APC da kuma Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ƙoƙarin yi wa shari’ar zaɓen shugaban ƙasa katsalandan, ta yadda za a iya bayar da nasarar zaɓe ga Bola Tinubu.
A wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran sa, Paul Ibe ya fitar, ya ce APC da Bola Tinubu na APC barazana ga shari’ar zaɓe.
Daga nan kuma ya ce, “ba a taba zaɓe mafi girman lalacewa kamar zaɓen 2023 ba.”
Ya ce Atiku za ya bi hanyar da ta dace domin hana a lalata dimoraɗyya.
An ruwaito cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya kira wayar Shugaban SSS da Babban Mai Shari’a, Ariwoola.
To amma kuma Shugaba ya ƙaryata zargin da Atiku ya yi, har Kotun Koli da APC sun ƙaryata zargin Tinubu ya kira Babban Alƙalin Tarayya ta waya.
Kotun Koli da kuma APC, sun ƙaryata zargin Tinubu ya kira Babban Alƙalin Tarayya ta waya, har suka yi taɓo yadda shari’ar zaɓen Shugaban Ƙasa za ta iya kaiwa.
An yi zargin Bola Tinubu ya kira Olukayode Ariwoola ta waya.
A cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labarai na Kotun Ƙoli ya fitar,
ya ƙaryata zargin cewa Bola Tinubu ya nemi Ariwoola ya sa wa hannu Yadda Kotun Ɗaukaka Ƙarar Zaɓen Shugaban Ƙasa ba ta soke zaɓen 2023
ba.
Ariwoola ke da alhakin bada hatta waɗanda za su yi shari’a a Kotun koli.
Ya ga dama ya naɗa wani ko shi da kan sa ya Shugabanci masu Shari’a.
Festus Akade, ya ce Ariwoola bai yi wata waya da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ba.
Daga nan ne kuma ya ce zargin Ariwoola ya yi waya da Shugaban SSS, ƙarya ce.
Ya ce shari’ar a fili a ke gudanar da komai. Saboda haka, kada a kawar da jama’a saurare.
Ya yi gargaɗin a daina amfani da kafafen watsa labarai akan watsa shirme a kafafen watsa labarai.
Shi kuma Kakakin APC, Felix Morka, ya ce masharranta kuma marasa gaskiya su ke yaɗa labaran ƙarya.
Kada a manta, a cikin Maris an yi zargin cewa Ariwoola ya gana da Bola Tinubu a Landan. Amma a lokacin ya fito ya ƙaryata.
Discussion about this post