Shugaba Bola Tinubu ya bayyana wa Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa cewa soke zaɓe don ba shi samu kashi 25% a FCT Abuja ba, molon-ka ne.
Ya bayyana haka a cikin rubutaccen ba’asi da ya yi na ƙarshe a shari’ar sa da Peter Obi na LP.
Ya ce FCT Abuja daidai ce da sauran jihohi, saboda haka batun soke zaɓe bata lokaci ne.
Peter Obi na LP ya garzaya kotu ya nemi kotu ta soke zaɓen Shugaban Ƙasa, saboda Bola Tinubu ya rasa samun 25% a FCT Abuja, da wasu dalilai.
Doka ta ce wanda ya yi nasara ya zama ya samu ƙuri’u ɗaya bisa ga uku na wasu jihohi, har da FCT Abuja.
Amma shi Obi ya ce tsarin mulkin Najeriya cewa ya yi tilas sai da FCT Abuja.
A bayanan Bola Tinubu da Wole Olanipekun lauyan sa ya gabatar, ya ce 25% a FCT Abuja ba dole ba ce.
Ya bayar da Sashe na 134 2b, ya ce a sashen babu wani wuri da aka ce lallai sai da FCT Abuja.
Shi ma ɗan takarar PDP, Atiku Abubakar ya garzaya kotu, ya nemi a soke zaɓen.
Dukkan su masu korafin sun kammala bayyana hujjojin su a kotu, a lokacin da lauyoyi ke ci gaba da daura damarar ganin sun kafa hujjojin da zai basu nasara a kotu a lokacin da za a yanke hukunci.
Discussion about this post