A ranar Litinin Babbar Kotun Tarayya ta dakatar da INEC gurfanar da tsohon shugaban Kwamishinan Zaɓen Adamawa, hudu Ari da ta samu da laifin bayyana zaɓen Gwamnan Jihar Adamawa ba da izni ba.
Mai Shari’a Donatos Olorowo ya yi dakatarwar, bisa riƙon da lauyan ‘yar takarar gwamnan Adamawa, Ɗahiru Banani ta yi.
Lauyan ta Michael Aondona ya ce wa kotu shari’ar da aka gurfanar da tsohon Ari za ta haifar da ruɗani ga shari’ar da ake yi tsakanin su da Gwamna Umar a Fintiri.
Dalilin haka ne su ke so a dakatar da shari’ar har zuwa bayan kammala ta su ɗin. Mai Shari’a ya amince da hakan.
Ko wancan lokaci, INEC ta yi fatali da sanarwar nasarar da Kwamishinan Zaɓe ya yi giringiɗishin cewa Binani ta APC ta yi, ta gayyaci Baturen Zaɓe da Kwamishina zuwa Abuja.
Hedikwatar Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi fatali da gaggawar bayyana sakamakon nasarar da Kwamishinan Zaɓen Adamawa ya ce Aishatu Binani ta yi.
Ari yi azarɓaɓin sanar da cewa Binani ce ta yi nasara, duk kuwa ba a kammala ƙidaya ba. Sannan kuma bashi ne wajibcin bayyana sakamakon zaɓe ya rataya a hannun sa ba.
“Azarɓaɓin da Kwamishinan Zaɓe na INEC na Jihar Adamawa ya yi ya bayyana nasarar wani ko wata ‘yar takara, ba abin amincewa ba ne. Saboda ba aikin sa ba ne, kuma ba a kammala haɗa ƙidaya ba.
“Saboda haka INEC na sanar da Baturen Zaɓe na Adamawa shi da Kwamishinan Zaɓe na jihar su gaggauta kawo kan su Hedikwatar INEC a Abuja, da gaggawa ana nan su.”
Sanarwar wadda Kwamishinan Wayar da Kai na INEC, Festus Okoye ya fitar a ranar Lahadi, kuma ta na ɗauke da bayanin sanarwar cewa Hukumar Zaɓe ta dakatar da komai wanda ya danganci sanarwar sakamakon zaɓen Jihar Adamawa.”
Safiyar Lahadi ne jaridar Daily Trust ta buga labarin cewa Kwamishinan Zaɓe na Jihar Adamawa Hudu Yunusa Ari, ya bayyana Aishatu Ɗahiru da aka fi sani da Binani cewa ita ce ta lashe zaɓen gwamnan Jihar Adamawa.
Kafin nan, an dakatar da tattara sakamakon zaɓe cikin dare jiya Asabar, aka ce sai washegari ƙarfe 10 na safiya, sai Kwamishinan Zaɓe ya bayyana cewa Binani ta APC ce ta yi nasara.
Ari ya yi wannan gangaci a lokacin da shi Baturen Zaɓe ba ya nan.
Sanarwar dai ta janyo ka-ce-na-ce a ɗakin tattara sakamakon zaɓen, cikin Adamawa da ƙasa baki ɗaya.
PDP ta nuna rashin amincewar ta ganin Kwamishina ne ya yi sanarwar, ba Baturen Zaɓe (R.O) ba.
Mele Lamiɗo wanda shi ne Baturen Zaɓe, ba ya cikin ɗakin tattara sakamakon zaɓen a lokacin da aka yi sanarwar.
Idan ba’a manta ba, tun a lokacin tattara sakamakon zaɓen da INEC ta ce bai kammalu ba na ranar 18 Ga Maris, sai da PDP ta yi ƙorafin cewa ba ta yarda ba kuma ba ta yi amanna da Haruna Ari ba.
A na su ɓangaren, tuni APC a Adamawa ta fara murnar nasara, kafin Hedikwatar INEC ta Ƙasa ta yi fatali da sanarwar.
Discussion about this post