Majalisar Dattawa ta amince wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ƙarasa daga inda tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya tsaya, ya amso bashin dala miliyan 800 domin raba wa talakawa milyan 12, waɗanda za a rika biya Naira 8,000 kowane wata, tsawon wata 6.
Waɗannan talakawan su milyan 12, za a raba masu 8,000 kowa har tsawon watanni shida.
Shugaba Tinubu ya bada tabbacin cewa idan aka bayar da rancen, za a rika tura kudaden Naira 8,000 duk wata zuwa asusun ajiyar bankin talakawa da marasa galihu miliyan 12 na tsawon watanni shida.
Shugaban kwamitin majalisar dattijai kan harkokin yada labarai da harkokin jama’a, Yemi Adaramodu, a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala zaman amincewa da wannan kudi, ya ce dala miliyan 800 din “Kudi ne na tallafi daga bankin duniya”.
Sanatoci da dama sun amince da gyaran dokar karin kasafin kamar yadda shugaba Tinubu.
Shugaban majalisar dattawa Gdswill Akpabio ya bayyana cewa bayan cire naira biliyan 500 daga cikin karin kasafin kudin, za a ware sauran kudaden kamar haka.
-N185,236,937,815 ga ma’aikatar ayyuka da gidaje domin rage tasirin ambaliyar ruwa da aka fuskanta a kasar nan a shekarar 2022 a shiyyoyin siyasa 6;
-N19,200,000,000 ga Ma’aikatar Aikin Gona ta Tarayya domin inganta barnar da aka yi wa filayen noma a fadin kasar nan a lokacin da aka yi mummunar ambaliyar ruwa a bara;
– Naira biliyan 35 ga majalisar shari’a ta kasa;
– Naira biliyan 10 ga Hukumar Babban Birnin Tarayya don gudanar da muhimman ayyuka; sai kuma
– Naira biliyan 70 ga Majalisar Dokoki ta kasa don tallafa wa yanayin aiki na sababbin mambobin.
Discussion about this post