A ranar Litinin din nan ce Majalisar Dattawa za ta fara tantance ministocin da Shugaba Bola Tinubu ya aika mata da sunayen su.
Tinubu ya zabo ministocin su 28 daga jihohi 25, wadanda suka hada da tsoffin gwamnoni hudu, tsoffin yan majalisar tarayya shida, mata bakwai da sauran su.
Kafin zuwan ranar tantancewar dai said a Gwamnatin tarayya ta umarce su cewa su je su yi rajista a Ofishin Babban Mashawarcin Shugaban Kasa a Fannin Harkokin Majalisa.
Kakakin Yada Labaran Majalisar Datttawa ya shaida wa manema labarai cewa a wannan lokacin za a tantance kowa ne yadda ya kamata, ba kawai mutum zai zo ya bayyana tarihin sa, ya yi gaba, shikenan ya zama minista ba.
Ya ce ba kowa za a zaba ya zama minista ba, sai mai halin kwarai, mai da’a, a cewar sa.
Akalla za a shafe kwanaki uku ana tantancewar a Majalisar Dattawa.
Yadda Ake Tantance Ministoci:
Da farko dai ‘Yan Majalisar Dattawa uku daga jihar da ministan ya fito ne za su fara gabatar da shi, ta hanyar nuna goyon baya gare shi, ko kuma gwasale shi, idan ba su goyon bayan sa.
Sai dai kuma idan tsohon sanata ne, ba za su yi masa tamboyoyin neman kure mutum ba. Sai dai su ce masa, ya yi gaisuwa ya tafi.
Wannan al’ada ce ake kallon ta na maida tantancewar kamar wani wasan yara.
Amma kuma idan akwai wadanda aka rubuto wani koke ko korafi a kan su, to akan yi ja-in-ja kafin a kai gaci.
Sabbin ‘Yan Ministoci Da Yankunan Da Suka Fito:
Kudu maso Kudu
Nyesom Wike – Rivers
Abubakar Momoh – Edo
Betta Edu – Cross River
Ekperikpe Ekpo – Akwa Ibom
Stella Okotette – Delta
John Enoh – Cross River
South-west
Olubunmi Tunji Ojo – Ondo
Dele Alake – Ekiti
Olawale Edun – Ogun
Waheed Adebayo Adelabu – Oyo
Kudu maso Gabas
Uche Nnaji – Enugu
Doris Aniche Uzoka – Imo
David Umahi – Ebonyi
Nkeiruka Onyejocha – Abia
Uju Kennedy Ohaneye – Anambra
Arewa maso Gabas
Yusuf Maitama Tuggar – Bauchi
Ali Pate –Bauchi
Abubakar Kyari – Borno
Sani Abubakar Danladi – Taraba
Arewa maso Yamma
Badaru Abubakar – Jigawa
Nasiru Ahmed El-Rufai – Kaduna
Ahmed Dangiwa – Katsina
Hannatu Musawa – Katsina
Bello Muhammad Goronyo – Sokoto
Arewa ta Tsakiya
Lateef Fagbemi – Kwara
Muhammad Idris – Niger
Iman Suleiman Ibrahim – Nasarawa
Joseph Utsev – Benue
Discussion about this post