An bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu zai fito da wasu sunaye 13 na wasu da za ya naɗa bayan waɗanda ya kai wa Majalisar Dattawa domin tantacewa.
Shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya fitar da sanarwar haka a ranar Alhamis.
A ranar ce aka fitar da sunayen 28 don a tantance.
Akwai Abubakar Momoh, Yusuf Tuggar, Ahmed Dangiwa, Hannatu Musawa, Uche Nnaji, Betta Edu, Doris Aniche Uzoka, David Umahi, da Nyesom Wike.
Saura Badaru Abubakar, Nasiru Ahmed El-Rufai, Ekperipe Ekpo, Nkeiruka Onyejocha, Olubunmi Tunji Ojo, Stella Okotette, Uju Kennedy Ohaneye, Bello Goronyo, Dele Alake, da Lateef Fagbemi.
Sai Muhammad Idris, Olawale Edun, Waheed Adebayo Adelabu, Iman Suleiman Ibrahim,. Ali Pate, Joseph Utsev, Abubakar Kyari, John Enoh, da Sani Abubakar Danladi.
Gbajabiamila ya ce “Tinubu zai sake fitar da wasu sunaye 13, zai ƙirƙiro ƙarin Ma’aikatu.
“Za a cire wasu ma’aikatu daga cikin waɗansu. Shi ya sa ba a faɗi a inda za a tura kowane sabon da za a naɗa ba.”
Discussion about this post