Majalisar dattawa ta kafa kwamitocin ta na musamman da na dindindin guda tara sannan kuma shi shugaban majalisar Godswill Akpabio, da mataimakinsa, Barau Jibrin, za su jagoranci kwamitin zaɓe da naɗe-naɗen kwamitocin majalisar.
Duka shugabannin majalisar mambobi ne na Kwamitin zaɓe da naɗe-naɗen kwamitocin Majalisar.
Sanata Akpabio ya bayyana naɗin sabbin kwamitin 9 ne a zauren Majalisar ranar Talata.
Akpabio ya kuma nada Sanata mai wakiltar Ogun ta Yamma, Ademola Olamilekan, a matsayin shugaban kwamitin kasafin kudi da kuma Bulalar Majalisa, sanata Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu, a matsayin mataimakin shugaba.
An nada Titus Zam, mai wakiltar mazabar Benuwe ta Arewa maso yamma a matsayin shugaban kwamitin dokoki da al’amuran majalaisar yayin da sanata Bamidele, zai kasance mataimakin shugaban kwamitin.
An nada Sunday Karimi mai wakiltar Kogi ta Yamma a matsayin shugaban kwamitin ayyuka na majalisar dattawa sannan Williams Jonah mai wakiltar Cross River ta tsakiya ya zama mataimakin shugaban kwamitin.
Okechukwu Ezea, wanda ke wakiltar Enugu ta Arewa kan tikitin jam’iyyar Labour Party (LP), shi ne zai shugabanci kwamitin da’a da korafe-korafe kuma Sanatan Kaduna ta Arewa, Khalid Mustapha ne zai taimaka masa.
An nada Aliyu Wadada, dan majalisar dattawa na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) mai wakiltar Nasarawa ta yamma a matsayin shugaban asusun shige da ficen kuɗaɗen jama’a da Nwebonyi Peter mai wakiltar Ebonyi ta Arewa a matsayin mataimakin shugaban kwamitin. Da ma kuma ita wannan kwamiti dan majalisar adawa ne ke jagorantar kwamitin bisa ka’idar majalisar.
An nada Shehu Umar mai wakiltar Bauchi ta Kudu a matsayin shugaban kwamitin kula da harkokin tsaro da leken asiri na kasa tare da Asuquo Ekpenyong mai wakiltar Cross River ta Kudu a matsayin mataimakin shugaba.
Sauran wadanda suka zama shugabannin kwamitoci sun hada da Garba Maidoki, Sanatan Kebbi ta Kudu, wanda aka nada a matsayin shugaban kwamitin kula da bin doka da oda da kuma Ede Dafinone na Delta ta tsakiya a matsayin mataimakin shugaban kwamitin.
Sanatan Ekiti ta Kudu, Adaramodu Adeyemi, shine shugaban kwamitin harkokin yaɗa labarai yayin da Shuaib Salisu mai wakiltar Ogun ta tsakiya zai kasance mataimakin shugaban kwamitin.
Sanata Akpabio bai faɗi sanda majalisar za ta naɗa sauran kwamitocin ba.
Discussion about this post