Gwamna Hope Uzodinma na Jihar Imo ya gana da Gwamnan jihar Legas, Baba Sanwo-Olu dangane da rushe wasu shagunan ‘yan ƙabilar su 17 a kasuwar Alaba, Legas.
Uzodinma ya tafi tare da tawagar ‘yan kasuwa ƙabilar igbo mazauna Legas.
Har a cikin waɗanda aka yi ganawar da su har da Ben Kalu na Majalisar Tarayya.
A makon jiya ne Gwamna Charles Soludo ya shawarci ‘yan asalin Jihar Anambra cewa ‘su dawo ku gina yankin ku, don ku tsira da mutuncin ku’.
Gwamna Charles Soludo na Jihar Anambra, ya shawarci ɗaukacin ƙabilar Igbo mazauna Legas cewa su maida hankali wajen bunƙasa jahar su, domin su tsira da mutuncin su.
Soludo ya yi wannan kiran a Legas tare da ‘yan asalin Jihar Anambra mazauna Legas, a taron da ya yi da su.
Sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna Soludo, Christian Aburime ya sa wa hannu, gwamnan ya halarci taron injiniyoyi ne a Jami’ar Legas.
“Matsawar ba ku gina yankin ku ba, to babu shakka a nan Legas ba za su kalle ku da daraja ba.” Cewar Soludo.
Soludo ya roƙi ‘yan Jihar Anambra cewa su daddage wajen tabbatar da haɓɓaka jihar Anambra.
“Wannan ce tambayar da a kullum na ke yi wa kai na. Saboda akwai haƙƙi a kan mu na habaka Anambra fiye da yadda mu ka same ta.”
Soludo ya yi wannan kiran ne biyo bayan rushe kanti 17 da Gwamnatin Legas ta yi, a Kasuwar Alaba, Legas.
Shagunan da aka rusa duk na ƙabilar Igbo ne.
Discussion about this post