A kalla mutum 50 ne aka kashe a rikicin da aka yi tsakanin kabilun Wurkuns da Karimjos a karamar hukumar Karamin Lamido jihar Taraba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Usman Abdullahi ya ce rikicin ya soma da misalin karfe ukun dare ranar Asabar a dalilin harin ramuwar gayya.
Abdullahi ya ce sanadiyyar rikicin mutane da dama sun ji rauni sai dai kuma rundunar ba ainihin adadin yawan mutanen da suka rasu.
Ya ce an kona gidaje, an kashe dabbobi sannan an kona gonakin mutane da dama a karamar hukumar.
“Rikicin ya samo asali a ramakon gayyan da kabilun Wurkuns da Karimjo ke kai wa juna.
Abdullahi ya ce rundunar tare da hadin gwiwar sojoji karamar hukumar ta fara samun zaman lafiya.
Ya ce wannan rikici ya sake barkewa ne mako daya da gwamnan jihar Agbu Kefas ya zauna da sarakunan gargajiya da manyan jami’an tsaron jihar domin magance matsalar tsaro a jihar.
A wannan zama, Kefas ya roki sarakunan su yi amfani da karfi su a matsayin shugabannin al’umma domin kawo zaman lafiya a jihar.
Wannan rikici dai ya barke ne tun bayan nadin sarauta da aka yi da wasu basu ji dadin haka ba.
Discussion about this post