Babban Kwamandan Askarawan Najeriya, Taoreed Lagbaja, ya bayyana cewa ba za a yi afuwa ga masu ta’addanci da garkuwa da mutane ba a Jihar Zamfara.
Ya bayyana haka ne a ziyarar da Gwamna Lawal ya yi masa, ranar Laraba a Abuja.
Ya ce a baya an yi afuwa ba ta yi amfani ba, amma ta ba masu ta’addanci damar ƙara ƙarfin hare-hare.
Lagbaja ya ce a Zamfara da kuma wasu wurare afuwa ba ta yi amfani ba, shi ya sa ya ce ba wata afuwa da za a yi wa ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga.
Ya ce ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin sojoji da gwamnatin Zamfara, an samu raguwar hare-hare a ƙauyuka da garuruwa a Zamfara.
A ganawar sa da Gwamnan Filato, Lagbaja ya ce Sojojin Najeriya za su magance rikicin jihar Filato.
Babban Kwamandan Askarawan Najeriya, Taoreed Lagbaja, ya jaddada cewa Sojojin Najeriya sun tsara hanyar magance rikicin jihar Filato.
Lagbaja ya bada wannan tabbacin a ziyarar da Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutwag ya yi masa, ranar Litinin, a Abuja.
Ya ce mafi yawan faɗace-faɗace a Filato matsala cewa tsakanin masu noma da masu kiwon a cikin wasu wurare.
Amma kuma ya ce wanda ya faru baya-bayan nan a Mangu, abin damuwa ne sosai ga sojoji da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.
“Tabbatar
maka cewa wannan matsala da ka kawo
inda ya fi dacewa a ɗaukar mata yadda za a iya magance ta.”
“Mun fito da wasu hanyoyi, waɗanda za a iya cewa an magance matsalar.”
Lagbaja ya ce Gwamna ya yi taro da masu ruwa da tsaki, domin a samu zaman lafiya, a bar tashe-tashen hankula.
Ya kuma shawarci Caleb da a fito da tsarin tsaro na cikin gida.
Haka kuma ya shawarci Gwamna ya fito da rahotannin baya, domin ya ga abin da ya dace a yi a baya, amma ba a yi ba.
Discussion about this post