Wata matar aure mai suna Latifa Musa ta roki kotun a Ilori jihar Kwara da ta raba aurenta da mijinta mai suna Kareem saboda rashin lafiya da barin ciki da take fama da su a koda yaushe.
Latifa ta bayyana cewa tun da suka yi aure da Kareem shekaru uku da suka wuce ta rika fama da tsananin rashin lafiya sannan kuma da bari a duk lokacin da ta dauki ciki.
Kareem bai halarci zaman kotu a ranar da kotun ta zauna ba da hakan ya sa alkalin kotun Aminullahi Abdullateef ya sa a aika wa Kareem samace domin ya gabatar da kansa a zama na gaba da kotun za ta yi.
Za a ci gaba da shari’ar ranar 14 ga Agusta.
Discussion about this post