Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa zai rika biyan ma’aikatan gwamnati a jihar naira 10,000 duk wata na tsawon wata shida domin rage radadin cire tallafin man fetur.
Shugaban ma’aikatan fada Edgar Amos ya sanar da haka ranar Laraba a garin Yola.
Amos wanda shine shugaban kwamitin da aka nada domin rage radadin cire tallafin man fetur a jihar ya ce gwamnati ta amince a rika biyan ma’aikatan jihar da sabon tsarin albashi daga watan Agusta.
Bayan haka Amos ya ce Fintiri ya amince a fito da tireloli 70 na nasara da 20 na shinkafa domin siyar wa mutane a jihar a farashin mai sauki.
Sannan gwamnati za ta siyar da buhunan takin zamani a farashin mai sauki wa ma’aikatan gwamnati a jihar.
Ya Kuma ce gwamnati ta Samar da manyan motoci da za su rika jigilan ma’aikatan gwamnati zuwa wuraren aiki daga gida.
Amos ya ce wadannan matakai da gwamnati ta dauka na daga cikin shawarwarin da kwamitin da aka kafa domin rage radadin cire tallafin man ta bada.
Discussion about this post