Maraimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam-Gwarzo ya karyata raɗe raɗin da ake ta watsawa wai gwamnatin Kano ta kudhe tsarin baiwa talakawa tallafin naira biliyan 500, wanda Tinubu ya ƙirkiro.
Sakataren gwamnatin Kano, Ibrahim Shuaibu ya sanar da haka a wata takarda da ta fito daga mataimakin gwamnan jihar ranar Asabar.
Sanarwar ta ce an yi wa kalaman mataimakin gwamnan mummunar fahimta ne, amma abin da ya ke cewa shine kokarin nuna wa ɗan jarida da yake hira da shi cewa akwai ɗan majalisa Sanata Alu Ndume da ya magana akan wannan tallafi.
” Abinda Abdussalam-Gwarzo ya ke nufi a nan shine karin bayani ya yi akan abin amma bai yi suka a kai ba. Shirin sa ake magana akai shiri ne da aka kirkiro ba tun yanzu ba, tun a mulkin baya aka tsara shi.
” Shi ma Tinubu ya samu wannan tsari ne, ba shine ya ƙirkiro abin ba.
A karshe Sakatare Shuaibu ya nanata cewa gwamnatin Kano karkashin gwamna Abba Yusuf, za ta na tare da shugaba Tinubu a dukkan ayyukan da gwamnatin sa za ta bijiro da shi don ci gaban jama’a.
Discussion about this post