Kwana uku bayan rantsar da Gwamna Abba Yusuf ya darzaza cikin birnin Kano da kewaye ya na rushe gine-ginen da ya yi alƙawarin rushewa a lokacin a yaƙin neman zaɓe.
Gine-gine ne da tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi watandar filayen su, ba bisa ƙa’ida ba.
Wannan tabbas gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje ta yi ɓarna babba, ta hanyar sayar da filayen asibitoci, makaranta da maƙabarta, ya riƙa raba wa manyan jami’an gwamnati, matar sa da ‘ya’yan sa.
To sai dai kuma ba a taɓa gyara barna da wata barnar. Don haka kamata ya yi Gwamnan Jihar ya fara aiki da kafa kwamitin binciken tantance masu Rajistar sayen filayen daga wurin Gwamnati.
Gwamnatin Ganduje ta yi kasassaɓar sayar da filayen maqabarta, makaranta, asibitoci, kasuwa,’ waɗanda Gwamnatin Abba ta bi ta kan su ta kwantar.
Sakataren Gwamnatin Abdullahi Baffa, ya ce za a karɓo kadarorin sama da tirliyan ɗayada Gwamnatin Abdullahi Ganduje ta sayar.
To, a halin yanzu wasu da aka rushe wa su na cewa sun bi tsari na doka.
Yayin da wata ƙungiya ta ce an yi asarar rayuka 25 sanadiyar rusau, ya kamata Gwamnati ta tsayar da rushewar, kamar yadda wata kotu ta bada umarni.
Ya kamata a gurfanar da Abdullahi Ganduje. Gwamnatin Kano ta yi daidai, amma rashin bada wa’adin tashi ya haifar da asara, ya rage wa gwamnatin armashi.
Discussion about this post