Bayan shafe shekaru da gwamnatocin Baya suka yi ana gallafiri da tattalin arzikin Najeriya, Gwamnatin Bola Tinubu ta yi gaba-gaɗin cire tallafin fetur, domin a samu yawaitar kuɗaɗen shiga.
Wannan sabuwar gwamnati ta bar Naira ta samar wa kan ta daraja a kasuwa.
Dama kowa ya san za a zo a wannan lokaci, bayan gwagwagwar sauya launin kuɗi da gwamnatin baya ta shigo da shi.
Amma kuma halin da ake ciki yanzu bayan cire tallafin fetur, ya sa tsadar rayuwa ta kai malejin wayyo, wayyo.
Ba batun tsadar rayuwar al’umma ta tsaya ba, hatta harkokin komai a cikin barazana da fargaba ake.
Wata matsalar wato adadin kuɗaɗen bashi da ake biya, ya zarce yawan adadin da ake samu.
Waɗannan matsalolin da suka yi tsaye cirko-cirko gefen tattalin arzikin Najeriya, babbar barazana ce ga hoɓɓasa da Bola Tinubu da fara domin gyara tattalin arzikin Najeriya.
Wasu masana cewa matsawar ba a rage yawan kuɗaɗen da gwamnati ke ragargaza ba, to tsarin garambawul a tattalin arzikin Najeriya ba zai yi tasiri ba.
Sabon garambawul ɗin tattalin arziki da Gwamnatin Bola Tinubu ke yi, ya nuna da farashin fetur da darajar kudaden mu duk a cikin kasuwa fahamin za a same shi.
To a gaskiyar magana a kan haka, farashin kayan masarufi kan tashi saboda yawan masu saye ya fi yawan abin da ake sayarwa.
Yayin da PREMIUM TIMES ta yarda cewa fasalin gyaran tattalin arzikin Najeriya da gwamnatin Bola Tinubu ta shimfiɗa abu ne mai ɗarsashi, to ba zai iya zama mai karsashi ba matsawar talakawa za su ci gaba da ɗaukar nauyin wahalhalun cire tallafin fetur, tsadar rayuwa, rashin aikin yi da rashin samun sassaucin ƙuncin rayuwa a Najeriya a halin yanzu, can gaba bayan shekaru masu yawa.
Discussion about this post