Majalisar Tsara Tattalin Arziki ta Kasa (NEC) ta umurci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da ta gaggauta raba hatsi ga jihohi nan da mako guda ko biyu domin karya farashin kayayyakin abinci a fadin kasar nan.
Ana fama da tsananin tsadar abinci da ma masarufi sanadiyyar cire tallafin mai da gwamnatin Bola Tinubu ta yi.
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron da majalisar tsara Tattalin arzikin kasa da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya jagoranta a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Alhamis.
Gwamnan ya ce Shettima ya umurci hukumar NEMA ta gaggauta sakin hatsin, inda ya kara da cewa jihohi su ma za su shiga cikin wannan shiri.
Gwamna Mohammed, ya nuna damuwarsa kan tsadar kayan abinci, ya kara da cewa abinci shine babban abin da majalisar ta yi la’akari da shi domin a samu sauki.
Muna da abinci danƙare a rumbunan hukumar NEMA, don haka majalisar ta ba da umarnin cewa nan da nan za a ware wa Jihohi kaso mai yawa na kayan abinci, hatsi da sauransu domin a rarraba su domin farashin kayan abinci ya karye, mutane su samu sauki.
“Za a ba da waɗannan hatsi a kan farashi kalilan. Bayan haka akwai shinkafa da ke ajiye wanda za a raba, wanda CBN ta sanar mana da su, cewa tun na shirin Anchor Borrowers ne da aka noma.
Gwamna Bala ya ce jihohi da da kananan hukumomi za su shiga gaba wajen raba hatsin da duka katan abincin da za a raba.
” Sannan kuma za ayi wannan rabon ne duka cikin makonni biyu kacal.
Discussion about this post