A taron da aka yi ranar Asabar, Kwamitin Raba Tallafin Fetur ya yi wa talakawa alwashin kashe masu ƙishirwa da rage masu raɗaɗin yunwa.
Shugaban Kwamiti, kuma Gwamnan jihar Kebbi, Idris ya ce kwamitin su za ya yi nasara da tabbatar da ganin ya fito da hanyoyin da talakawa za su samu tallafin saboda cire tallafin fetur da aka yi.
Sauran waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Gwamna Bala Mohammed daga Bauchi, da wasu Gwamnonin Najeriya.
PREMIUM TIMES ta bada rahoton talakawa milyan 12 za a rika biya Naira 8,000 kowane wata, tsawon wata 6.
Majalisar Dattawa ta amince wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ƙarasa daga inda tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya tsaya, ya amso bashin dala miliyan 800 domin raba wa talakawa milyan 12, waɗanda za a rika biya Naira 8,000 kowane wata, tsawon wata 6.
Waɗannan talakawan su miliyan 12, za a raba masu 8,000 kowa har tsawon watanni shida.
Discussion about this post