Matsalar tsaro ta na ci gaba da addabar Katsina, yayin da ‘yan bindiga suka jidi manoma a Nahuta, Madogara, Zamfarawa, Dadare da Ɗantsuntsu da sanyin safiya.
An kwashe su a lokacin da suke gona a ƙaramar hukumar Batsari.
Wani Ma’aikacin Kiwon Lafiya a Ɗantsuntsu, ya ce da dare ya yi an nemi manoma 35, an rasa.
Ya ce da sanyin safiya aka bi ana kamawa, har aka kama 10 a garin su.
An tafi da maza, mata da yara da aka yi gaba da su daga gonar su.
“An tafi da wani yaro mai shekaru 12, wanda ba ya
iya tserewa.”
‘Yan sanda a Katsina sun ce manoma 14 aka sace.
“An tafi da mutum 14 a Madogara, Ma’aikata na ta bincike.”
Discussion about this post